Tsofaffi sun mamye siyasar Afirka
August 1, 2025Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa wani dogon sharhi kan siyasa mai taken: "Tsofaffin nahiyar Afirka na son ci gaba da mulki", inda ta ce shugabanni da dama da suka haura shekaru 80 na kara tsayawa takara, duk da adawar da ke karuwa a tsakanin al'umma. Jaridar ta ce na farko shi ne Paul Biya na Kamaru mai shekaru 92, wanda ya kasance shugaban kasa mafi tsufa a duniya, kuma yana mulki tun shekarar 1982. Na biyu shi ne Yoweri Museveni mai shekaru 80, wanda ya dare kan kujerar mulki tun 1986. Shi kuwa na uku na da shekaru 83, Alassane Ouattara, kuma yana nema wa'adi na hudu na mulki ba bisa ka'ida ba.
Karin Bayani:Jaridun Jamus: Takarar Biya ta dauki hankali
Neue Zürcher Zeitung ta ci gaba da cewa, takarar shugabannin Kamaru da Yuganda da Côte d'Ivoire a zaben watanni masu zuwa ba alama ce mai kyau ga tsarin dimukuradiyya a nahiyar Afirka ba. Dalili kuwa shi ne, babu wata nahiya da ke da tsofaffin a matsayin shugabanni kamar nahiyar Afirka. Abin mamakin ma shi ne, da yawa daga cikinsu na daukar kansu a matsayin haske da ba za a iya maye gurbinsu ba duk da shekaru da dama da suka shafe a mulki. Jaridar ta ce zabubbukan uku da aka yi hasashen sakamakonsu na nuna yadda yanayin dimukuradiyya ke da rauni a nahiyar Afirka da ke da kasashe 54.
Su kuwa jaridun Frankfurter Allgemeine Zeitung da Faz.Net sun mayar da hankali ne kan mace-macen masu zanga-zanga a Angola a lokacin da ke nuna fushinsu kan cire tallafin man fetur. A sharhin da ta yi, Faz.Net ta ce ba kasafai ake gudanar da zanga-zanga a Angola ba, amma bayan da aka soke tallafin mai, bore ya ta'azzara inda akalla mutane hudu suka mutu yayin da aka kama daruruwan masu zanga-zanga. Jaridar ta tunatar da cewa Angola ce kasa ta biyu wajen fitar da mai a Afirka bayan Najeriya, amma take ci gaba da shiga da mai daga waje saboda rashin ingantattun matatun mai.
Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce abin da ya faru a Angola na da makancecniya da zanga-zangar nuna adawa da karin farashin man fetur sakamakon cire tallafi a Najeriya shekara guda da ta wuce. jaridar ta ce mutane da yawa na fargabar cewar karin farashin sufuri zai sa kayan abinci da sauran kayayyaki su yi tsada. Amma maimakon ya magance abin da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya, shugaban kasar Angola João Lourenço, ya zargi masu zanga-zangar da yin amfani da tsadar man fetur a matsayin hujja wajen yi wa gwamnati zagon kasa.
A nata bangaren die tageszeitung ta tofa albarkacin bakinta kan matsalar karancin abinci a nahiyar Afirka a karkashin sharhinta mai taken: "'Yunwa na raguwa, amma ba a ko'ina ba", inda ta ce sabon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce a daidai lokacin da aka ja wa 'yunwa birki a wasu sassa na duniya, lamarin ya sha bamban a Afirka da Gabas ta Tsakiya sakamakon rikice-rikice da matsalar sauyin yanayi. Jaridar da ake wallafawa a kullum ta ce yayin da adadin masu fama da 'yunwa a duniya ya ragu a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2024, adadin ya ninka a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka daga miliyan 68 zuwa 140.
Die tageszeitung ta ci gaba da cewa, a kasashe 'yan rabbana ka wadata mu na Afirka, lafiyayyen abinci na da tsada idan aka kwatanta da sauran sassa na duniya. Kuma sakamakon hauhawar farashin masarufi da aka fuskanta a shekarar 2024 a Afirka, fiye da kashi biyu bisa uku na mutane sun rage adadin abincin da suke ci a kullun, kama daga unguwar marasa galihu na Nairobin Kenya zuwa na Ghana, lamarin da ke mummunan tasiri a tsarin kiwon lafiyarsu.