Tserewar masu taɓin hankali a Kenya
May 13, 2013'Yan sandan Kenya sun shiga sintirin neman wasu masu taɓin hankali 40 da suka tsere daga wani asibitin mahaukata mai suna Mathari, wanda ke babban birnin ƙasar wato Nairobi.
Kamfanin dillancin Jamus ya rawaito cewa masu fama da taɓin hankalin sun yi kokuwa da masu tsaronsu ne har suka ci ƙarfinsu suka yi ficcewarsu.
A shekarar 2011 masu rajin kare haƙƙin bil adama sun yi kira da a gudanar da bincike kan asibitin bisa zarginsu da tabka laifuka na cin zarafin bil adama, bayan da gidan talabijin na CNN ya gabatar da wani rahoto mai tayar da hankali, wanda ya gwado irin yanayin da masu taɓin hankalin ke rayuwa a asibiti.
'Yan sanda sun ce masu taɓin hankalin sun yi zanga-zanga kafin suka ɗauki matakin tserewar.
Mathari shine asibitin mahaukata mafi girma a kenya, kuma baki ɗaya, asibitin na da majinyata 75.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh