Tsananin zafi a kudancin Turai
Da zafin da ya kai sama da digiri 40 a ma'aunin Celsius a Girka da Italiya da Turkiyya da Cyprus, batun yawon bude ido ya tsaya cak yayin da jami'an kashe gobara ke fafutukar shawo kan gobarar daji da ke ruruwa.
Akwai matsanancin zafi
A Athen babban birnin kasar Girka, ana rufe manyan wuraren tarihi kamar Acropolis a lokutan tsananin zafi saboda kare lafiyar masu yawon bude ido da ma'aikatan da ke musu rakiya. Wani matashin mai shekaru 18 a duniya da ya zo daga Amurka, ya bayyana cewa bai shiryawa wannan zafin ba yana mai cewa: "Ba yanayi ne mai dadi ba a yanzu, amma na sabarwa da kaina shan ruwa sosai."
Cikin tsananin zafin rana
A Girka da Macedoniya ta Arewa, ana fama da yanayin da ya kai digiri 40 a ma'aunin Celsius. Mahukunta na gargadin al'umma kan illar tsananin zafin, tare da ba su shawarar zama a gida. Idan kana aiki a waje, zafin na da matukar illa ga jiki. Victor ke nan da ke aiki a matsayin dan rakiya ga masu yawan bude ido a birnin Skopje na Macedoniya, yana zuba ruwan sanyi a fuskarsa.
Kura da Toka
Wajen linkaya a tsakiyar konannun gidaje, a kauyen Souni da ke Cyprus. Daruruwan mutane na kwana a sansanonin wucin-gadi, sakamakon gobarar daji. Jiragen sama na kashe gobara na kawo dauki daga Jordan da Isra'ila da kuma Spain, zuwa tsibirin domin kashe wutar dajin. Wutar ta mamaye kimanin kilomita 120, na dazuzzukan wannan tsibiri.
Wajen sanyaya jiki a Sicily
An samar da gulbi na ruwan sanyi a birnin Catania da ke Sicily, inda wannan mutumin ya je domin samun sa'ida. Tuni mahukuntan Palermo babban birnin Tsibirin na Sicily, suka yi gargadin samun tsananin zafi. A yankin Apulia na Italiya, mahukunta sun sanar da mutuwar mutane biyar da ke da alaka da matsanancin zafin da ka iya zama barazana ga rayuwar yara kanana da tsofaffi.
"Babu Inuwa"
A birnin Rome masu yawon bude ido na fakewa a karkashin inuwar lemarsu, yayin da suke jiran masu yi musu rakiya zuwa muhimman wuraren tarihi. A wasu lokutan, masu yawon bude ido na faduwa saboda kishirwa sakamakon tsananin zafi. Mamba a kungiyar Federagit ta masu yin rakiya ga masu yawon bude ido a birnin Rome Francesca Duimich ya tabbatar da hakan, inda ya ce: "Babu inuwa kuma babu iska."
Sanyaya jiki a Santanbul
Fadawa cikin kogin Bosporus da ka, hanya mafi sauki wajen sanyaya jiki a birnin Santanbul na Turkiyya. Tsananin yanayin zafi "na sahara" na dauko iska mai zafi daga Afirka zuwa yankin Tekun Bahar-Rum. A Turkiyya tuni yanayin ya kai sama da digiri 40 a ma'aunin Celsius, a yankuna 18 na kasar. Masana yanayi, sun yi hasashen cewa tsananin zafin zai ci gaba da karuwa.
Yankin Balkan na cin wuta
Jami'an sa-kai a kauyen Ponor da ke kusa da Sofia babban birnin kasar Bulgeriya, na haka ramuka da nufin samar da hanyoyi da za su taimaka wajen kashe gobarar a gabar ruwa domin hana wutar dajin da ke ruruwa shiga gonaki da kuma yankunan da mutane ke zaune.
Aiki cikin Tsananin Zafi
Saka kayan aiki daga sama har kasa cikin tsananin zafi, ba abu ne mai sauki ba. A Sofia babban birnin kasar Bulgeriya, ma'aikaci da ke yin talla na tsaye sanye da alamar kayan kwalam da makulashe. Bayan mutuwar wani ma'aikaci da ke irin wannan tallan a birnin Barcelona, muhawara ta barke kan bai wa ma'aikata kariya. Kungiyoyin kwadago, na bukatar a bai wa ma'aikata kariya sosai a lokacin bazara.
Lokacin bazara kan iya zama abin sha'awa
A lokacin maraice mai cike da yanayi na dumi, yara da matasa na wasa cikin ruwan sanyi. An shawarci ma'aikata a Girka, su rage lokutan aikinsu a lokacin bazara tare da daukar hutu yayin cin abincin rana. Sai dai hakan, ba tilas ba ne.