Tsananin sanyi a Turai ya janyo asarar rayuka
February 5, 2012Masu hasashen yanayi sun yi gargaɗin cewa tsananin sanyin wanda ya karaɗe tun daga Italiya zuwa yankin Baltic zai cigaba da ƙaruwa har zuwa ƙarshen mako. Tsananin sanyin mafi muni shine a ƙasar Ukrain inda mutane 101 suka rasa rayukansu. A Jamhuriyar Czech sanyin ya kai awo 38 ƙasa da sufili a ma'aunin Celsius. A ƙasar Bulgariya kuwa sassa da dama na kogin Danube ya daskare saboda tsananin sanyin yayin da a ƙasar Italiya ma jami'ai suka ce ƙoramar Venice ta fara daskarewa. A ƙasar Estoniya ma an bada rahoton wani mutum da aka samu mace a gefen hanya a Talinn babban birnin ƙasar. Haka ma dai a ƙasashen Latviya da Lithuaniya an sami rahotannin jikata a sabili da sanyin. A halin da ake ciki kuma rahotanni daga ƙasar Belgium na cewa zubar dusar ƙanƙara ta haddasa tsaikon ababen hawa har tsawon kilomita dubu da ɗari ɗaya.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal