Tsadar rayuwa cikin mulkin Faye a Senegal
April 2, 2025Duk da tallafin CFA biliyan 73 biliyan da ya ware wa fannin masarufi, har yanzu matsalar tsadar rayuwa na ci gaba da addabar al'umma da ke jiran samun kyautatuwar yanayin rayuwarsu.
Tallafin kayayyakin bukatun yau da kullun na daga cikin matakan farko da Bassirou Diamaye Faye ya dauka bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Senegal a Afrilun 2024. Sai dai har yanzu ba a rabu da Bukar ba a kasar ta yammacin Afirka, saboda ana ci gaba da fusakntar hauhawar farashi a kasuwannin Senegal. Amma dai, an samu daidaituwar farashin wasu kayayyaki musmaman ma masarufi, in ji Fatou Mbodj Pouye, shugabar La Casamançaise, kungiyar tattalin arziki da ta kware a fannin sarrafa kayayyakin amfanin gona.
Fatou Mbodj Pouye, ta ce: "A wannan shekarar mun samu rangwamen farashin shinkafa, albasa, dankali, kai dai duk abubuwan da suka shafi albarkatun noma. Amma muna fuskantar matsalolin tattalin arziki na karancin kudin shiga da kuma matsalolin da suka shafi kayan aiki, wanda ba ko yaushe ake samun su ba. Cinikin da muke ya yi kasa idan aka kwatanta da bara."
Farashin iskar gas da ruwan fanfo da wutar lantarki da kudin haya da sufuri da sauran ayyukan yau da kullun bai sauka ba a shekarar farko ta mulkin Diamaye Faye a Senegal. Saboda haka ne kungiyoyin da ke kare hakkin masu sayen kayayyaku suka shawarci gwamnati da ta nuna gaskiya kan yanayin tattalin arzikia kowane mataki, in ji Jean-Pierre Dieng, shugaban kungiyar masu amfana da ayyukan gwamnatin Senegal. Sannan, ya koka da rashin tuntubar jama'a wajen aiwatar da hanyoyin samar da rangwame a matsalar hauhawar farashin kayayyakin yau da kullum.
"A game da abin da ya shafi magidanta, dole ne a dama da kungiyoyin da ke kare hakkin masu sayan kayayyaki a duk abin da gwamnati ta yi da kuma take son yi a nan gaba, amma a matsayin hadin gwiwa. A gare mu, babu wata hujja ta zahiri da ke nuna cewar alkalumman da gwamnati ta gabatar game da tallafin kayan abinci na da gamshin gaskiya, sakamakon yadda aka tafiyar da kudin kasa a baya, za a iya sa 60 maimakon 100."
Hauhawar farashin kayayyakin yau da kullum a Senegal ta kai kusan kashi 7.2%, a cewar Hukumar Kididdiga ta kasa (ANSD). Amma ga masanin tattalin arzikiSeydina Oumar Séye, hauhawar farashin da ake fuskanta duk da tallafin CFA biliyan 73 da gwamnati ta zuba na dalilai guda biyu. Na farko tsarin kudin kasar da hauhawar farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga waje. A cewar masanin dai, wannan yanayin tsadar masarufi zai iya ci-gaba har tsawon wasu shekaru masu zuwa.
Seydina Oumar Séye ya ce: "A cikin watanni goma sha biyu, ba daidai ba ne a yi kokarin cimma burin katse hauhawar farashin kayayyaki. Zai dauki tsakanin shekaru uku zuwa biyar kafin a cimma sakamakon da ake so. Sannan a cikin gajeren lokaci, ya zama dole a ware tallafi ga wasu takaitattun kayayyaki, wato, a yi amfani da fasahar zamani don kauce wa yin sama da fadi da kudin da aka tanada."
Gwamnatin Senegal ta yi alkawarin kara rage farashin kayayykin albarkatun da aka fi amfani da su a shekara ta 2025.