Trump ya zargi Rasha da kin kawo kashen yakin Ukraine
July 5, 2025Wannan furuci ya nuna babban sauyi, domin a baya Shugaba Trump ya yi ikirarin cewa Putin na son kawo karshen yakin da ya kaddamar kan Ukraine a 2022.
A ranar Alhamis, Rasha ta kai wani babban hari da jiragen sama marasa matuki a Ukraine, sa'o'i kalilan bayan tattaunawa tsakanin Trump da Putin wanda aka ce ta neman kawo karshen yakin ce.
A ranar Juma'a, Shugaba Trump ya kuma yi magana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, inda suka tattauna batutuwan makaman kariya ta sama da kuma karuwar hare-haren Rasha.
Trump ya sanar a wannan makon cewa za a dakatar da isar da makamai masu linzami samfurin Patriot na Amurka zuwa Ukraine domin kiyaye ajiyar makamai na cikin gida.
A lokaci guda, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya nuna sha'awar sayen wadannan makaman kariyar ta sama don taimaka wa Ukraine.