Amurka za ta gudanar da ayyukan tashoshin makamashin Ukraine
March 20, 2025A ci gaba da kokarin sulhunta rikicin da ke tsakanin kasashen Rasha da Ukraine da ke makwabtaka da juna, shugaban Amurka Donald Trump yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Shugaba Volodmyr Zelensky, ya ce kasarsa za ta iya taimakawa wajen gudanar da ayyuka a tashoshin makamashin Ukraine. Wannan tayin dai na zuwa ne a yayin da tawagar Ukraine ke shirin fara tattaunawa a Burtaniya domin samar da wata rundunar sojojin wanzar da zaman lafiya karkashin jagorancin mahukuntan kasashen Turai.
Shugaba Zelensky ya bayyana cewar Ukraine a shirye take ta dakatar da kai farmakinta a kan tashoshin makamashin Rasha da sauraran ababen more rayuwa domin kawo karshen wannan yakin da aka kwashe sama da shekaru uku ana gwabza shi. Burtaniya da Faransa sun sha alwashin samar wa Ukraine da tsaro mai dorewa a kasar musamman a tashoshin makamashinta.
A ranar Laraba Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni sama da 350 albarkacin shiga tsakanin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi.