SiyasaJamus
Amurka za ta iya kai hari na biyu kan Iran
June 27, 2025Talla
Trump ya ce idan har jami'an leken asirin Amurka sun tabbatar cewa Iran na ci gaba da inganta shirinta na nukiliya, babbu shakka za su sake daukar wani sabon mataki.
Tun farko Amurkar da Israila sun ce sun lallata tashoshin nukiliya na Fardo da Tanz a hare-haren da suka kai. To amma daga bisannin jagoran adinin Iran Ayyatollah Khomeni ya ce ko kadan tashoshin ba su lalace ba.