Za mu kai wa Iran harin idan tattaunawa ta ci tura - Trump
March 30, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar yin amfani da tsinin bindiga a kan Iran muddin tattaunawa da fadar mulkin ta Teheran ta ci tura kan shirin kasar na nukiliya.
A wata hira da gidan talabijin na NBC ya yi da shi a wannan Lahadi, shugaba Donald Trump ya ce idan Iran ta ki rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ake kokarin yi da ita, ba makawa Amurka za ta yi mata ruwan bamabamai.
Trump ya kuma kara da cewa a yanzu haka jami'an Amurka da na Iran sun hau kan teburin tattauna sai dai bai yi karin haske ba kan cikin irin yanayin da ake musayar yawun, sannan kuma ta bayyana yiwuwar kara labta wa Teheran karin takunkumai.
Karin bayani: Iran ba za ta tattauna da Amurka kan mamakin nukuliya ba
A tsakiyar wannan mako dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ya jaddada matsayar Teheran na bijerewa tattaunawa kai tsaye da Amurka karkashin matsin lambar shugaba Trump da kuma barazanar daukar matakin soja a kan kasar.