Trump ya yi barazanar maka jaridar Wall Street a kotu
July 18, 2025Shugaban Amurka Donal Trump ya sanar da aniyarsa da maka jaridar Wall Street a gaban kotu kan wata wasika mai kunshe da zanen badala da ta danganta da shi, wadda aka aike wa attajirin Amurka Jeffrey Espein a 2003. Trump ya kuma karyata jaridar ta Amurka tare da bayyana labarin da ta yada a matsayin kage da kuma tozarci.
A wani da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Mista Trump ya ce jaridar ta Wall Street ta yada labarin karya da mugunta da batanci, yana mai tabbatar da cewa idan har da da kanshin gaskiya a cikin lamarin da tun tuni abokan hamayyarsa na siyasa sun yi amfani da labarin a matsayin makami domin yakarsa.
Shi dai Jeffrey Epstein attari ne a Amurka wanda aka samu gawarsa ya rataye kansa a dakinsa na kurkuku a ranar 10 ga watan Ogusta na 2019, kafi yi masa shari'a kan zargin aikata laifuka na yin lalata da mata.