Trump ya sha alwashin karin kaso 50 na haraji kan Kanada
March 11, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shirin rubanya harajin kudin fito kan karafuna da dalma da ke shiga kasarsa daga Canada.
A yanzu Trump ya ce Canada za ta rika biyan kashi 50% na haraji kuma matakin ya biyo bayan da Ontario ta lafta kaso 25% ne kan wutar lantarki da ke zuwa daga Amurkar.
Sabon harajin Amurka kan Canada da Mexico ya fara aiki
Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa ya fada wa sakataren harkokin kasuwancinsa daga Ranar Laraba da safe, a maka wa Canada karin kaso 25% na haraji.
Trump ya lafta harajin kaso 25% ga karafa dake shiga Amurka
Shugaban na Amurka ya kuma rubuta a shafin nasa cewa dole Canada ta dakatar da haraji kan manoman Amurka na kashi 250%.
Tun a lokacin da ya sha rantsuwar kama kama ne Trump din ya yi alkawarin lafta haraji kan kasashen Canada da Mexico da kuma China.