Trump ya sauya sunan ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon
September 6, 2025Talla
A lokacin da yake jawabi a offishinsa, shugaban Amurka Donald Trump ya ce sauya sunan a yanzu shi ne mafi daidai ta la'akari da yadda duniya ta sauya kuma sauyin na isar da sako ne na yin nasara. Kana sunan zai nuna irin karfin da rundunar sojin kasar take da shi. A cewar Sakataren harkokin tsaron kasar, gwamnatin Amurka na son nuna cewa ta na yi da gaske wajen kare kanta. A yanzu dai Shugaba Trump ya ce za su mika sauyin sunan a gaban Majalisar dokokin kasar idan akwai bukatar ta amince.