SiyasaAmurka
Ana dab da cimma yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza
July 2, 2025Talla
Trump ya bukaci kungiyar Hamas da ta amince da shirin yayin da sojojin Isra'ila ke fadada kai hare-hare a yankin Falasdinu.Shugaban na Amurka ya rubuta a dandalin Truth Social, cewa Isra'ila ta amince da sharuddan da suka dace don tsagaita bude wuta na kwanaki 60.
Inda za su yi aiki tare da dukkan bangarorin domin kawo karshen yakin, amma ba tare da ambato sharudan ba, Yakin da ya samo asali sakamakon wani hari da Hamas ta kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, na shekara ta 2023.
ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da dubu 50 galibi farar hula kawo yanzu, yayin da wasu 'yan Isra'ila sama da dubu suka mutu: