Trump ya lafta harajin kashi 100% ga fina-finan Hollywood
May 5, 2025Trump ya ce hakan ya faru ne sakamakon kasashen da ke bai wa masu shirya fina-finan Amurka damar gudanar da harkokinsu a farashi mai rahusa wanda hakan kuma ke haifar da mummunar koma baya tare kuma da durkusar da Hollywood da ta yi sharafinta a shekarun baya.
Karin bayani: Bikin baje kolin fina-finai a Berlin: Sabbin fina-finan Afirka sun dauki hankali
Shugaban ya kuma bada umarnin gaggawa ga Ma'aikatar Kasuwanci ta Amurka da ta gaggauta aiwatar da wannan doka ta tilasta wa Amurkawa shirya fina-finansu a cikin gida ko kuma su fuskanci harajin kashi 100% ba tare da bata lokaci ba.
Karin bayani: An fara shari'ar Donald Trump kan zargin bada toshiyar baki
Matakin Amurkan na zuwa ne wata guda da China ta sanar da cewa za ta rage adadin fina-finan Amurka da ake shigarwa kasarta.