Trump ya kare matsayin karbar jirgin Qatar
May 12, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya kare shirin gwamnatinsa na karbar kyautar jirgin sama na alfarma sabo fil kirar Boeing bayan da kafofin yada labarai suka ruwaito cewa Iyalan gidan sarautar Qatar za su ba shi kyautar Jirgi domin maye gurbin jirgin shugaban kasa Airforce One.
Gidan talabijin na ABC News ya baiyana jirgin Dangarama kirar Boeing 747-8 da cewa fada ce a cikin jirgin sama kuma mai yiwuwa wannan ita ce kyauta mafi tsada da aka taba bai wa gwamnatin Amurka.
Masu sukar lamiri sun ce karbar irin wannan kyauta na iya saba tsauraran dokoki kan kyautuka ga shugabanni da ma sanya ayar tambaya kan cimma muradu na radin kai tsakanin harkokin kasuwancin Iyalan Trump da kuma amfani da matsayinsa a gwamnati.
Trump dai na shirin kai ziyara kasashen Saudiyya da Qatar da kuma hadaddiyar Daular Larabawa daga ranar Talata zuwa Alhamis na wannan makon.