SiyasaAmurka
Trump zai shirya taro tsakanin Putin da Zelensky
August 19, 2025Talla
Shugaban na Rasha ya amince da taron da ake sa ran za a yi nan da makwannibiyu masu zuwa, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Amurka, in ji shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, daya daga cikin jami'an Turai da aka gayyata zuwa fadar White House. ga kuma abinda yake cewa :
''Tattaunawar gaske za ta iya gudana ne, kawai a taron kolin da Ukraine za ta shiga . Irin wannan taron ba zai yiwu ba, ba tare da tsagaita wuta ba. Shin Shugaban na Rasha zai cika alkawarin shiga wannan taro ban sani ba:''