Trump ya fusata da Isra'ila kan dakile shigar da agaji Gaza
June 9, 2025Shugaban Amurka Donald Trump na shirin tattaunawa da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a wannan Litinin, sakamakon fusata da ya yi kan matakan Isra'ila na dakile shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza na Falasdinu.
Wasu jami'ai biyu na fadar White House, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Mr Trump ya gargadi Netanyahu da kada ya bata shirin da Amurka ke yi na kulla yarjejeniya da Iran, wajen ganin ta jingine shirinta na habaka makamin kare dangi na nukiliya, wanda tattaunawar cimma masalaharsa ta yi nisa.
Karin bayani:Isra'ila ta karkata akalar jirgin ruwan da ke kai agaji Gaza
A kwanan nan ne Iran za ta mika wa Amurka sabon tayin cimma yarjejeniyar ta hannun kasar Oman, wanda ya yi hannun riga da muradan Amurka, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya sanar a wannan Litinin.