Trump ya ce zai soke yarjejeniyoyi da EU da wasu kasashe
September 4, 2025Talla
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce kasarsa na iya tilasta soke yarjejeniyoyin kasuwanci da ta kulla da Tarayyar Turai da Japan da Koriya ta Kudu da ma karin wasu kasashe, muddin ta sha kaye a shari'ar kotun koli a game da halaccin harajin da ya kakaba a baya-bayan nan.
Yayin taronsa da shugaban Poland, Karol Nawrocki, Mr. Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa na rokon kotun koli da ta rusa hukuncin kotun daukaka kara na Amurka da aka yanke cikin makon da ya gabata, wadda ta ce yawancin harajin da ya kafa ba su da tushe a doka.
Wannan jawabi na Trump shi ne na farko da ke nuni da yiyuwar a soke yarjejeniyoyin kasuwanci da manyan abokan huldar Amurka idan kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara.