Amurka da China sun dakatar da harajin da suka dora wa juna
August 12, 2025Talla
Trump ya bayyana haka ne a danlinsa na Truh Social na sada zumunta gabanin wa'adin farko da ya kaide ya kare cikin sao'i kadan.
Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya rawaito ma'aikatar kasuwanci ta kasar China, ita ma tana mai sanar da dakatar da karin haraji kan kayayyakin Amurka na tsawon kwanaki 90.
A watan Mayun da ya gabata ne, Washington da Beijing suka yi; ta yin sa-in-sa, a kan harajin da ya kai kashi 145 kan kayayyakin kasar China da kuma kashi 125 kan kayayyakin Amurka.
Kafin daga baya su samu masalha wacce ta yi ragi da kashi 30% na haraji kan kayayyakin kasar china, yayin da, a kann kayayyakin Amurka ya kai kashi 10%.