SiyasaArewacin Amurka
Trump ya ce akwai yiwuwar mataimakinsa ya gaje shi a 2028
August 6, 2025Talla
Trump ya sauya matsayi kan kin amsa makamanciyar tambayar da aka yi masa a watan Fabrairu kan waye zai gajeshi, wajen ci gaba da yada manufofin gwamnatin Amurka da ake yiwa lakabi da 'Dawo da ruhin Amurka' wato Make America Great Again (MAGA).
Karin bayani:Donald Trump na neman tazarce
Kalaman shugaban na zuwa a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan furucin Trump din na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin samun wa'adin mulki a zango na uku.