Trump na Amurka zai gana da Zelenskiy na Ukraine
August 18, 2025Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy da shugabannin Turai za su gana da Donald Trump na Amurka a Washington a yau Litinin domin tsara yarjejeniyar zaman lafiya, yayin da ake fargabar cewa shugaban Amurka na iya matsa wa Kyiv lamba ta amince da yarjejeniyar da za ta amfani Moscow.
Gabanin ganawar ta yau shugaba Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa Ukraine ta mance da zancen shiga kungiyar tsaro ta NATO kwata-kwata.
Kasashen Turai na matsin lamba ga Amurka kan tabbatar da tsaron Ukraine
Shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Burtaniya da Jamus da Faransa da Italiya da kuma na Finland na fatan karfafa wa Zelenskiy gwiwa a wannan muhimmin lokaci na diflomasiyya a yakin.
Har ila yau, suna fatan hana maimaituwar irin ganawar sa insa tsakanin Trump da Zelenskiy kamar yadda aka gani a watan Fabrairu.
Trump zai fara ganawa da Zelenskiy da karfe 5:15 GMT sannan daga baya ya zanta da dukkan shugabannin Turai da misalin karfe 7:00 agogon GMT, in ji Fadar White House.
Makomar yakin Ukraine na hannun Zelensky -Trump
Bayan ganawarsa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Alaska a ranar Juma'a, Trump ya ce ya kamata a cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin da ya dauki tsawon watanni 42 ana fafatawa.