Trump: Karin haraji na cike da kalubale
April 10, 2025Talla
Trump da ke jawabi a yayin wani taron da ya jagoranta a fadar White House, kana a kwana guda bayan ya sanar da jinkirta matakin harajin har nan da watanni uku masu zuwa, ya kara da cewa siyasar tasa ka iya haifar da wasu matsaloli, to amma kuma daga karshe Amurka ce za ta ci gagarumar riba, kuma hakan zai kasance mata babban alheri.
Kasar China ce dai shugaba Donald Trump ya fi laftawa kudin harajin, inda ya ce za ta biya har kaso 125 cikin 100 na kudaden karin harajin, bayan da ya jinkirta hakan ga sauran kasashe har tsawon watannin uku.