Trump da shugaban Koriya ta Kudu za su gana a White House
August 12, 2025Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Kudu Lee Jae Myung za su gana a birnin Washigton DC a ranar 25 ga watan Augustan 2025, domin tattauna al'amuran da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki.
Karin bayani:Kamfanonin kera motocin Koriya da Japan sun fara jin radadin harajin Trump
Fadar shugaban kasar Koriya ta Kudu ta sanar da cewa shugabanin biyu za su sake yin nazari kan alakar diflomasiyyar da ke tsakaninsu tare da shimfida sabuwar taswirar tattalin arziki da tsaro.
Karin bayani:Sabon shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae-myung ya sha rantsuwar kana aiki
Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Koriya Kang Yu-jung ta ce dangane da yarjejeniyar haraji da aka cimma tsakanin Washington da Seoul a watan Yuli, shugabannin biyu za su fadada kasuwancin na'urorin latironi da kayan masana'antu da kimiyya da fasaha da dai sauransu.
A nata bangaren, Amurka ta bukaci Koriya ta Arewa da ta kara kudin da take kashewa kan dakarunta daga dala biliyan daya.