Shugaba Trump da al-Sharaa za su yi ganawar keke da keke
May 14, 2025Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Siriya Ahmed al-Sharaa za su yi ganawar keke da keke, sa'o'i bayan sanar da matakinsa na janye takunkuman karayar tattalin arziki da aka kakaba wa Siriya shekaru da dama.
Shugaban Siriya na ganawa da shugabannin kasashe
Donald Trump da ke ziyarar aiki yankin Golfe, ya sanar da matakin soke takunkuman ne, a lokacin da yake jawabinsa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, inda ya bayyana cewa hakan zai ba wa Siriya damar haskawa da sake tsintar kanta cikin wani yanayi na sabon numfashi
EU za ta janye wa Syria takunkumin karya tattalin arziki
Tun a gabanin matakin Donald Trump, kasashen duniya da dama ciki har da na nahiyar Turai, sun rangwamta tsauraran takunkuman da suka kakaba wa Siriya, bayan da Shugaba al-Sharaa ya kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamban 2024.
Al'ummomi a manyan biranen Siriya sun kwana da kade-kade domin nuna murna kan matakin na Amurka wanda suke fatan ganin zai sawaka musu rayuwa