Togo: Yan mata na katse karatu saboda juna biyu
March 20, 2025Farko dai babbu wani kudirin doka a cikin kasashen da ya haramta wa burduwar da ta dauki ciki daina zuwa makaranta ko daukar darasi amma duk da haka yawancin yara mata suna barin karatun saboda matsin lamba na zamantakewa da na iyali da suke fuskanta.
Claire Mathieux matashiya wacce ta samu kanta a cikin irin wannan hali ta haifi danta a tsakiyar shekarar karatu ana saura watanni biyu a yi jarabawa ta tsaida yin karatu. Ta dade tana boye halin da take ciki, saboda tsoron yadda ‘yan uwanta za su kalleta
Ban samu kwarin gwiwa ba wajen fada a gida halin da nake ciki amma mahaifiyata ta lura cewa ba ni da lafiya. A matsayinta na uwa, ta gane alamun cewa ina dauke da juna biyu, dole na sanar da ita a lokacin ta kira mahaifina ta shada masa wanda cikin fushi ya yi mini duka da guduma.
Bayyanai na hukuma a kasar Togo sun nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, an yi rajistar masu juna biyu 8, 631 a tsakiyar shekarar karatu
Duk yawancin wadannan yara ‘yan mata makomarsu ta fada cikin rashin tabbas Michelle Aguey wata lauya ta ce kamata ya yi kotu ta rika hukunta mazan da ke yi wa ‘yan matan da ke karatun ciki
"Wannan lamari ne mai damuwa. Yawancin lokaci, an fi son sasantawa. Wanda ke da alhakin yi wa yarinyar ciki sau da yawa ya dara ta da shekaru. An fi bada fifikon cewa a tattauna kan cewar zai iya daukar nauyin yarinyar da yaron. Matsi na zamantakewa ya hana aiwatar da doka ko wani bi ma doimin ana jin tsoron wanda ya yi cikin ko mai gata ne.''
Doka dai a sashinta na 19 na dokar kare hakkin ‘yan makaranta masu kankantar shekaru ta ce, babban mutumin da ya mallaki hankalinsa da ya yi wa karamar daliba ciki, za a iya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara daya zuwa biyar tare da tarar CFA miliyan biyar. Amma duk da haka a mafi yawan lokuta, dokar ba ta aiki saboda kamun kafa na dangi da yan uwa